Jamus: Matakai kan sinadaran kashe kwari
November 6, 2018Talla
Kasashen Turai da Amirka sun jima suna tabka muhawara bisa zargin Sinadarin Glyposate na kamfanin Bayer AG da haddasa cutar sankara. A watan Fabrairun wannan shekara ne dai Jam'iyyar CDU wacce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke jagoranta tare da SPD Jam'iyyar hadaka suka amince da hanin amfani da sinadarin na Glyphosate ko da ya ke ba a sanar da da lokaci ba. A halin yanzu dai ministar muhallin ta tabbatar da cewar hanin amfani da sinadarin a kusa da ruwa da sauran gurare ya fara aiki kuma zai cigaba da aiki har zuwa shekara ta 2023 lokacin da dokar haramcin amfani dashi za ta fara aiki.