1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus na juyayin wadanda corona ta kashe

April 18, 2021

Jami'an gwamnatin Jamus sun yi zaman makokin jajenta wa juna a kan asarar da kasar ta yi na dubban 'ya'yanta sanadin annobar cutar corona da duniya ke fama da ita.

https://p.dw.com/p/3sByx
Coronavirus | Berlin Kaiser-Wilhelm-Gedächtnis-Kirche | Gedenken für Covid-Opfer
Hoto: Gordon Welters/Pool KNA/AP/picture alliance

Jamus ta gabatar da addu'o'i na kasa a yau Lahadi, musamman saboda kusan mutum dubu 80 da annobar corona ta yi sanadin su daga bara i zuwa halin da ake ciki.

Taron addu'o'in da aka yi ya jingine duk wata jayayyar da ake da ita game da matakan da aka dauka na yaki da yaduwar cutar a kasar.

Shugabar gwamnati Angela Merkel da Shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier tare da wasu jagorori ne suka hadu a majami'ar Kaiser Wilhelm da ke Berlin, inda aka gudanar da addu'o'in.

Haka nan ma an yi zama a Konzerthaus duk dai a Berlin din inda Shugaban kasar Steinmeier zai gabatar da jawabi ga wadanda suka rasa nasu sakamakon kamuwa da corona.

Galibin Jamusawa dai za su kallin yadda bikin zai gudana ne ta akwatunan talabijin, ganin taro ne da ba zai hada mutane da yawa ba saboda gudun yada cutar.