Jamus na shakku kan kawancen NATO
March 1, 2017Talla
Ministan ya kuma kara da cewar 'yan siyasa su kan yi alkawuran da ba za su iya cikawa ba daga baya, don haka yana ganin ba dai-dai bane a yanke wani adadi a ce shi ake da bukata. Su dai kasashen kawance na kungiyar tsaro ta NATO, a wani taro da suka yi a shekara ta 2014, sun amince a kan dukkan kasashen kawancen za su rika kashe kaso biyu na tattalin arzikin su a kan harkokin tsaro har zuwa shekara ta 2024.
Ko da yake ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta soki lamirin wannan tsokaci na ministan harkokin wajen kasar, wanda aka yi a wajen taron kasa da kasa da aka yi a birnin Munich jim kadan bayan ya yi gargadi a kan batun mayar da hankali akan harkar tsaro kawai.