Shirin mayar da kayan tarihi Najeriya
April 30, 2021Wasu daga cikin kayan tarihin wadanda aka sace tun a karni na 19 suna ajiye a gidajen tarihi a nan Jamus. A ranar Alhamis ne shugabannin kula da al'adu da na siyasar Jamus suka cimma yarjejeniyar mayar wa Najeriya kayan tarihin daga shekara mai zuwa.. Kayan tarihin na masarautar Benin da ke kudancin Najeriya sojojin Birtaniya ne suka kwaso su a lokacin da suka afkawa masarautar a shekarar 1897.
Kayayyakin na karni 16 da karni na 18 wadanda suka hada da kayan kira da sassake sassaken katako da aka kawata fadar masarautar Benin na daga cikin kayayyakin tarihi masu daraja na Afirka. Wadannan kayayyaki a yanzu sun warwatsu a gidajen tarihi a kasashen turai.
Bayan cimma yarjejeniyar amincewa da mayar da kayayyakin, mataki na gaba shi ne tsara jadawalin yadda za a mayar da kayayyakin shirye shiryen da za a kammala nan yan watanni masu zuwa.
Hakan dai na nufin daukar kididdigar dukkan kayayyakin nan da ranar 15 ga watan Juni sanann a sake bitar matakan a ranar 29 ga watan na Juni.
Jamus dai ta bada muhimmanci gaske wajen hadin kai da kasashen Afirka kan gidajen adana tarihi. Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya baiyana yarjejeniyar da aka cimma a matsayin muhimmin bigire a yadda kasar ke tafiyar da al'amuranta na tarihin mulkin mallaka.
Maas yace sun dade tsawon watanni suna aiki tukuru domin samar da kyakkyawan yanayi na wannan aiki. Yana mai cewa Jamus ta sanya batun kawance kan gidajen tarihi da Afirka a jadawalinta na zamantakewar siyasa tare da neman tattaunawa da abokan huldarsu na Najeriya wadanda suka kafa gidan tarihin na Benin akan batutuwa kama daga kawance a fannin kayan mutan da, da bada horo ga manajojin kula da gidan tarihi da kuma taimako kan alkinta kayan tarihin duk an tsara su kuma ana cigaba da aiki akan haka.
Ministar kula da al'adu ta Jamus Monika Gruetters ta ce suna fatan bada gudunmawa ga samun fahimtar juna tare da sasantawada ahalin wadanda aka sace kayansu na tarihi a zamanin mulkin mallaka.
Hermann Parzinger na gidauniyar al'adu ta Prussia yace manufa dai ita ce mayar da kayayyakin nan da shekara ta 2022. Yace an shirya tattaunawa da takwarorinsu na Najeriya yadda za a tabbatar da dawo da kayayyakin cikin nasara da kuma kulla kawancen hadin kai a gaba.
Wannan ya hada da tattaunawa akan yadda za a bar wasu daga cikin kayayyakin domin baje kolin su a gidajen tarihi na Jamus.
Muhimman kayayyakin tarihin dai suna nan a gidajen adana kayan tarihi na Jamus. Misali akwai kayayyaki kusan 530 na masarautar Benin a gidan tarihin dake Berlin wadanda suka hada da kayan kira na tagula kimanin 440.
Matsin lambar da aka yi ta yi akan turawan mulkin mallaka a 'yan shekarun baya na dawo da kayan tarihin da aka sace daga Afirka ya fara tasiri.
A watan da ya gabata Jami'ar Aberdeen a Scotland ta amince za ta dawo wa da Najeriya wani sassaken tagula na masarautar Benin tana mai cewa sojojin Birtaniya ne suka kwaso kayayyakin a 1897 a wani yanayi na tursasawa.
Wannan mataki ya kara kaimi ga sauran cibiyoyi ciki har da gidan tarihi na Birtaniyasu bi sahu wajen dawo da kayan tarihin da aka sace.
Najeriya na fatan gina katafaren gidan tarihi a birnin Benin domin adana kayayyakin da aka sace bayan an dawo da su wanda zai ci kudi euro miliyan uku da dubu dari hudu wanda Birtaniya za ta tallafa.
A bara Faransa ta amince za ta dawo da kayayyaki guda 26 wadanda aka dauke daga masarautar Bini a 1892.