1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 5 da harin kasuwan Krismeti

Ramatu Garba Baba
December 19, 2021

Shugaba Frank-Walter Steinmeier zai jagoranci taron tuni da wadanda suka rasa rayukansu a yayin wani harin ta'addanci da aka kai kan kasuwan Krismeti shekaru 5 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/44Woo
Hanau Anschlag 2020 | 1. Jahrestag Rückblick | Gedenken
Hoto: rheinmainfoto/imago images

A wannan Lahadin al'ummar Jamus ke taron adduo'i don tunawa da mutanen da suka mutu a sakamakon wani harin ta'addancin da aka kai kan kasuwan Krismeti na birnin Berlin shekaru biyar da suka gabata. Shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier ne zai jagoranci taron.

Mutum kimanin goma sha daya ne suka mutu a yayin da wasu akalla saba'in suka jikkata a harin. Gabanin cika shekaru biyar, dangin wadanda abin ya shafa sun rubuta wata wasika zuwa ga gwamnatin tarayya domin baiyana rashin gamsuwa a game da yadda gwamnati ta gudanar da binciken harin inda suka nemi a karrama wadanda suka tsira daga harin.

Wani dan kasar Tunisiya mai suna Anis Amri, wanda ya gaza samun mafaka a Jamus ne, ya kutsa da wata babbar motar da ya sato cikin dandazon mutane a kasuwan da ke Berlin babban birnin kasar a kasuwan da ke ci a duk watan Disamba, maharin ya soma harbe direban motar. Kwanaki bayan kai harin ne jami'an tsaro a kasar Italiya suka yi nasarar harbe maharin da ya tsere daga Jamus bayan aika-aikan.