SiyasaJamus
Jamus ta samar da daftarin dokar corona
April 22, 2021Talla
Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya rattaba hannun kan sabuwar dokar da za ta bai wa gwamnatin kasar damar aiwatar da dokar hana yaduwar annobar corona. Amincewa da dokar a hukumance, na nufin dokar za ta yi aiki a dukkan wuraren da ake samun yaduwar annobar a jihohi 16 na tarayyar kasar
A dai jiya Laraba, 'yan majalisar dokokin Jamus, suka kada kuri'a kan daftarin shawarwari da Shugabar gwamnati Angela Merkel ta gabatar, wanda zai tilasta daukar matakin na bai daya, domin dakile cutar corona a wuraren da annobar ke yaduwa cikin gaggawa, dokar za ta cigaba da aiki har zuwa karshen watan Yuni. Dubban masu adawa da daftarin yaki da coronar na ci gaba da baiyana adawarsu, inda suka ce matakin ya ci karo da 'yancin dan Adam.