Jamus ta ce za ta iya da 'yan gudun hijira
August 23, 2016Tambayoyin da DW ta nemi amsoshinsu daga 'yan kasar kenan. A shekara ta 2015 ne dubban 'yan gudun hijira maza da mata da yara mafi akasari daga Siriya da Afghanista da Iraki suka samu shiga kasar Jamus ta kasashen yankin Balkan, bayan da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ayyana kudurinta na karbar 'yan gudun hijirar a karshen watan Augustan bara. Kalmarta ta "za mu iya" ta yi tasiri ga cimma manufofinta.
Shin ko kudurin ya sauya kasar Jamus, in ko hakane to ta yaya? Daga ranar 15 zuwa 17 ga wannan wata na Auguta, DW ta kaddamar da wata cibiya domin kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta: "Infratest Dimap polling institute" domin jin ta bakin 'yan kasar da suka cancanci kada kuri'a su akalla 1,000. An mika bayanai guda hudu dangane da tsarin karbar 'yan gudun hijirar ga wadanda suka kada kuri'ar, inda aka tambayesu shin za su amince ko kuma kin amincewa da wadannan bayanai.
Tsarin karatu da harkokin more rayuwa.
An kiyasta cewa abin da za a kashe wajen tallafawa 'yan gudun hijirar ya kai kimanin biliyan 15 na kudin Euro, a ko wace shekara. Da fari duk wanda ya iso za a ba shi masauki da kuma abinci. Sauya musu tsarin rayuwa zuwa irin tsarin rayuwar Jamusawa, zai yi wu ne kawai idan sun koyi harshen Jamusanmci, kana kuma suna da ilimi. Ana bukatar malaman da za su koyar da su da kuma wadanda za su koyar tare da kula da yaraansu a makarantun nazare da firamare. Shin wannan ka iya kara yawan kudin haraji da Jamus ke samu da ma shafar yanayin rayuwar 'yan kasar? Wasu daga cikin wadanda aka ji ra'ayinsu na da ra'ayin haka.
Batun samun karuwa a fannin ilimi da ma rayuwar 'yan kasa abin damuwa ne, a cewar magoya bayan jam'iyyar adawa ta Alternative for Germany AfD a Jamus da ke rajin kishin kasa. Kimanin mutane 15 cikin 100 na jam'iyyar ta AfD da suka amsa tambayoyi yayin jin ra'ayin jama'ar basu amince da wannan kalami ba.
Batun tattalin arziki
Ga wanda ke jin harshen Jamusanci, kuma mai zurfin karatu da lafiyar jiki, abu ne mai sauki samun gurbin aiki a Jamus Jamus na fuskantar kalubalen rashin yawan matasa majiya karfi, mutane na kara tsufa kana suna barin aiki, sai dai babu isassun matasa da zasu maye gurbinsu. Wannan shi ne abin da mafi yawan kamfanoni ke fuskanta.
Ga ko wanne mutane 100 da basu da aikin yi a Jamus, akwai kimanin gurbin kwararrun ma'aikata 200 da ake nema, shin ko 'yan gudun hijira da bakin haure ka iya cike wadannan gurbi?
Amsar ba mai sauki bace. A Jamus fannin injiniya a bangaren kanikanci da masana'antun kera motoci da kuma injiniya a fannin hasken wutar lantarki ne ke samar da kaso 20 cikin 100 na tattalin arzikin kasar. Wadannan kamfanoni basu damu da kasashen da mafiya yawan bakin hauren da 'yan gudun hijira suka fito ba, a sabo da haka zai yi wuya su samu gurbin aiki a wadannan masana'antu. Duk da haka wasu daga cikin wadanda aka ji ra'ayinsu nada ra'ayin cewa bakin hauren na da rawar takawa wajen bunkasa fannin tattalin arzikin Jamus din.
Dangane da tambayar da ta shafi tsarin karatu da da rayuwar Jamusawa kuwa, kaso tara cikin 10 cikin magoya bayan jam'iyyar AfD ta masu kishin kasa da suka bayyana ra'ayoyinsu na ganin cewa ba bu wata riba da shigowar 'yan gudun hijira da bakin haure Jamsu za ta haifar. Sai dai ra'yin nasu ya sha ban-ban ga mafi yawan 'yan siyasa da matasa da masu zurfin ilimi da kuma masu kudi cikin Jamusawa, wadanda ke da ra'ayin cewa 'yan gudun hijira da bakin hauren za su karaffafa tattalin arzikin Jamus din. Koda yake mutanen da suka haura shekaru 50 a duniya da kuma wadanda basu yi ililmi mai zurfi ba basu yarda da hakan ba.
Jamus ta fara zama ba ta Jamusawa ba?
Zuwan 'yan gudun hijira Jamus ba wai zai shafi fannin tattalin arzikin kasar bane harma da yanayin zaman takewa. Jamus kasa ce data kasance masauki ga 'yan kasashen ketare masu yawa musamman a manyan biranenta. hakan na iya karuwa nan gaba. Ko me Jamusa ke tunani kan wannan ci gaban?
A nanma siyasa na taka muhimmiyar rawa, matasan Jamusawa da kuma Jamusawan da ke da ilimi mai zurfi ka iya yin maraba da al'umma mai "al'adu daban-daban." Haka kuma ga alamu su ne suka yi watsi da dangantakar da ke tsakanin tsarin karbar 'yan gudun hijirar na Merkel da kuma batun karuwar hare-haren ta'addanci a kasar. Sai dai wadanda suka manyanata da kuma wadanda basu da ilimi mai zurfi da aka ji ta bakinsu na da ra'ayin cewa Jamsu ka iya fuskantar hare-haren ta'addanci masu yawa a nan gaba.
Kazalika a kan wannan batu, ko hadakar siyasa ba shi da mahimmanci. Anan ma dai Matasa da Jamusawa masu zurfin karatu ne suka yi maraba da zamantakewar dakar al'adu. Kuma su din ne suka yunkuri kin amincewa da kudurin Angela Merkel na karbar baki da yawaitar ayyukan ta'addanci da kasar ya fuskanta. Masu yawan shekaru cikin wdan da suka amsa tambayoyin da masu karancin karatu na da yakinin cewar Jamus ka iya fuskantar karin wasu haren ta'addanci a nan gaba. To amma sai dai ansamu sabani ra'Ayin siyasa dandane da wannan tambayar, inda kashi bakwai cikin mutane 100 ne daga cikin magoya bayan jam'iyyar 'yan ra'ayin rikau ke da ra'ayin Jamus ba za ta fuskanci wasu hare-haren ta'addanci anan gaba ba.
Hare-haren ta'addanci nan gaba?
Ra'ayin 'yan siyasa a nan ya karkata wani bangare daban, kimanin kaso bakwai na magoya bayan AfD ne kacal ke da ra'ayin cewa ba za a kara samun hare-haren ta'addanci a Jamus na gaba ba.