1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta damu da dabi'un Trump

July 18, 2018

Kasar Jamus ta nuna damuwa da dabi'un shugaba Trump wadanda suka shafi huldarsa da kasashe.

https://p.dw.com/p/31fLG
Deutschland Aussenminister Heiko Maas
Hoto: picture alliance/dpa/S. Schuldt

Gwamnatin kasar Jamus ta bayyana rashin tabbas dangane da yadda shugaban Amirka Donald Trump ke tafiyar da harkokinsa da kasashen waje.

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, ya ce kasar na bukatar samun yanayi na tabbas daga Shugaba Donald Trump, musamman ganin yawan tufka da warwara da ake gani cikin tsukin sa'o'i 24 kacal da Donald Trump ke yi kan muhimman batutuwa da suka danganci diflomasiyya.

A cewar Heiko Maas, yayin wata ganawar da ya yi da takwaransa na kasar Chile Roberto Ampuero yau a birnin Berlin, abu ne mai matukar daure kai yadda mr Trump ke maganganu masu karo da juna.

Shugaban na Amirka da ake iya cewa yana da yawan katobara, ya lashe wani amai da ya yi, bayan wata ganawar da ya yi da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan zargin Rashar da marar hannu a zaben Amirka na baya, abin kuma da ya harzuka Amirkawa matuka.