Jamus ta hana kona tutar Isra'ila yayin gangami
December 11, 2017Ministan harkokin cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere ya yi alawadai da kone-konen tutar Isra'ila a yayin gangamin mara baya ga Falasdinawa da aka yi a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, bayan da Amirka ta bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila. Jamus dai na da tata alakar ta fiska ta daban da kasar ta Isra'ila da ma al'ummar Yahudawa kamar yadda de Maiziere ya fada wa jaridar Bild da aka buga a wannan rana ta Litinin.
A cewar de Maiziere ba za su lamunta ba a rika amfani da irin wannan dama ana tozartawa ga Yahudawa ko Isra'ila.
An dai kona wasu tutoci na Isra'ila guda biyu a ranar Juma'a a gaban ofishin jakadancin Amirka da ma gaban kofar nan mai tarihi ta Brandenburg da ke a tsakiyar birnin Berlin. Wannan dai na zuwa bayan da Shugaba Trump na Amirka ya bayyana sauya matsayar birnin Kudus zuwa babban birnin Isra'ila.
An dai kama mutane 10 wadanda 'yan sanda ke zarginsu da kona tutar wata kasar waje. Har ila yau a ranar Lahadi ma an sake kona wata tutar a gangamin da kimanin mutane 250 suka fita a birnin na Berlin a yankin Neukoelln da Kreuzberg. De Maiziere ya ce Jamus na da matsayarta kan batun na birnin Kudus amma cin mutuncin wata kasa ba da su ba.