Haramcin shiga Jamus ga wasu 'yan Saudiyya
November 19, 2018Talla
Hukumomin Jamus sun haramta shiga kasar ga 'yan Saudiyya 18 da ake zargi suna da hannu wajen kashe dan jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Samtanbul na Turkiyya. Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya tabbatar da haka a wannan Litinin a wajen taron kungiyar Tarayyar Turai a birnin Brussels na kasar Beljiyam.
Ranar biyu ga watan jiya na Oktoba aka hallaka Jamal Khashoggi, wanda ya kasance mai sukar Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gadon sarautar Saudiyya. Tun bayan faruwar lamarin masarautar Saudiyya ta shiga matsin lamba na kasashen duniya kan neman hukunta wadanda suke da hannu kan kisa gami da wanda ya ba da umurni, da ake kyautata zaton shi kansa Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gadon sarauta.