1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ja hankalin kasar Libiya

December 8, 2017

Gwamnatin Jamus ta bukaci gwamnatin kasar Libiya ta bai wa kungiyoyin agaji na duniya damar shiga sansanonin 'yan gudun hijira da ke kasarta.

https://p.dw.com/p/2ozhz
Berlin Merkel und Libyscher Premierminister Fayez al-Sarraj
Angela Merkel tare da Fayez al-Sarraj a birnin BerlinHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Sohn

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci gwamnatin kasar Libiya ta bai wa kungiyoyin agaji na duniya damar shiga sansanonin 'yan gudun hijira da ke kasarta domin kai dauki da dubban Afrikawa dake makale a kasar. Angela Merkel ta nuna bukatar hakan ne, lokacin wata ganawar da ta yi da firaministan Libiya Fayez al-Sarraj a birnin Berlin. Hakan dai na zuwa bayan wasu rahotannin sun yi nunin mummunar yanayi da wasu bakin haure bakar fata suke ciki a Libiyar.

Firaministan na Libiya ya yi alkawarin maganta matsalar da bakin haure ke ciki, yanan mai cewa Libiya ta tsara wasu ofisoshin da ke aikewa mayar da matasan Afirkawan kasashen da suka fito. Haka nan ma ya tabbatar da yadda tuni wasu kasashen suka soma kwashe mutanensu da suka makale a Libiyar.