1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta samu gurbi a kwamitin sulhu

Zulaiha Abubakar
January 1, 2019

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya baiyana shirin kasar na nemo mafita a matsalolin da kasashen duniya ke fama da su daidai lokacin da kasar ta fara waadin shekaru biyu a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya

https://p.dw.com/p/3Aru2
UN Sicherheitsrat Yemen
Hoto: Reuters/C. Allegri

Heiko Maas ya kara da cewar Jamus ta shirya tsaf don fuskantar kalubalen da ke gabanta.Taraiyar Jamus dai ta zamo daya daga cikin kasashe 10 da suka sami wakilcin karba karba a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar bayan kasashen Faransa da Rasha da Birtaniya da Chaina da Amirka wadanda ke da kujerun dindindin a kwamitin sulhun. Kare mata da yara kanana a yankunan da ake yaki da batun muhalli da kuma tsaron lafiyar ma'akatan agaji a kasashen dake rikici na daga cikin kudirorin kasar ta Jamus a kwamitin tsulhun Majalisar Dinkin Duniyar.