1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta nuna damuwa da kalaman Abbas

Abdullahi Tanko Bala
August 17, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya baiyana damuwa da kalaman shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas kan kisan kiyashi da aka yi wa Yahudawa.

https://p.dw.com/p/4FfPg
Berlin | Pressekonferenz: Olaf Scholz und Mahmoud Abbas
Hoto: Wolfgang Kumm/dpa/picture alliance

A wannan Laraba gwamnatin ta gayyaci babban jami'in diflomasiyya a ofsihin jakadancin Falasdinawa da ke Berlin domin nuna rashin jin dadi da yadda shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya kwatanta matakan Isra'ila da kisan kare dangi.

Kakakin gwamnatin Jamus ya ce a baiyane yake ga gwamnatin Jamus da shugabanta cewa azabtarwa da kisan gillar da aka yi wa Yahudawa miliyan shida a Turai mummunan laifi ne na cin zarafin dan Adam wanda ba zai misaltu ba ballantana a yi kwatance da shi.

A yayin ziyarar da ya kawo Berlin a ranar Talata shugaban na Falasdinawa ya zargi Isra'ila da aikata kisan kare dangi har sau hamsin yayin da yake mayar da martani ga wata tambaya da aka yi masa game da bikin cika shekaru 50 na harin da wasu tsagerun Falasdinawa suka aka kai wa tawagar Isra'ila yayin gasar Olympics a birnin Munich a shekarar 1972.