1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Turai sun soki matakin Isra'ila

Suleiman Babayo MNA
July 24, 2019

Kasashen Turai musamman Jamus da Faransa da Birtaniya sun soki matakin Isra'ila na rushe gidajen Falasdinawa a gabashin birnin Kudus da ake gani zai tabarbara shirin samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin.

https://p.dw.com/p/3MdnP
Israel beginnt, Häuser am Stadtrand von Jerusalem abzureißen
Hoto: Reuters/M. Qawasma

Kasashen Jamus, da Faransa gami da Birtaniya sun yi kakkausar suka kan matakin gwamnatin Isra'ila na rushe gidajen Falasdinawa a gabashin birnin Kudus. A cikin wata sanarwar mambobin kasashen Tarayyar Turai sun suna rashin jin dadin abin da ke faruwa wanda suke ce ya janyo radadi ga talakawan Falasdinawa, da janyo nakasu kan shirin samar da zaman lafiya.

Ranar Litinin da ta gabata Isra'ila ta dauki matakin fara rushe-rushen gine-ginen a kauyen Sur Baher, wanda ke karkashin ikon hukumar cin gashin kan Falasdinawa. Sai dai gwamnatin Isra'ila ta kare matakin da cewa yankin da aka yi gine-ginen na cikin inda aka shata a matsayin inda ya raba sassan biyu, kana sabbin manyan gine-ginen 12 sun saba ka'ida kan iyaka tsakanin Isra'ila da yankin gabar yamma da kogin Jordan.