Jamus ta yabawa Musulman kasar
May 12, 2021Talla
Steinmeier ya nuna juyayi kan yadda za su gabatar da bikin cikin tsauraran matakan hana yaduwar cutar corona a karo na biyu. Sai dai ya ce da alamun haske a allurar rigakafin annobar da ake sa ran za ta kawo karshen wahalhalun da aka fuskanta.
A sakonsa ta faifan bidiyo, Steinmeier ya kuma mika godiyarsa ga musulman Jamus bisa yadda suka jajirce wajen bin dokokin annobar na takaita haduwa tun daga watan Maris din bara. A nan Jamus ma a ranar Alhamis take ranar karamar sallah. Alkalumma na nuna cewa kimanin musulmai miliyan 4 ne ke zaune a Jamus.