Jamus ta yi wa Facebook tarnaki kan bayanai
February 7, 2019Kamfanin na Facebook dai yace zai daukaka kara kan wannan tarnaki yana mai cewa hukumar sa ido kan gogayyar kamfanoni na kasar Jamus ba ta fahimci girman kalubalen da Facebook din yake fuskanta ba.
Hukumar sa ido kan goggayar kamfanonin ta dauki matakin yiwa Facebook tarnaki ne bayan wani hukunci da kotu ta yanke a wannan Alhamis wanda ya nuna cewa kamfanin na Facebook ya wuce gona da iri wajen tattara bayanan masu amfani da shafukansa.
Shugaban hukumar lura da gogayyar kamfanonin na Jamus Andreas Mundt, yace daga yanzu ba za a bar kamfanin Facebook ya tilasta wa masu amfani da shafukansa wajen bada bayanansu ba, yana mai cewa kamfanin zai iya amfani ne da bayanai daga sauran shafukan da ba na Facebook ba da kuma manhajar da ya mallaka kamar WhatsApp da Instagram idan ya sami amincewar masu amfani da shi.
A yanzu dai Facebook na hade galibin bayanan da ya samu na masu amfani da shafukansa ne bai daya.