Jamus: Tantance masu neman mafaka a wata kasa
June 21, 2024Talla
Daga cikin matakan da gwamnatin ke nazari sun hada da yarjejeniyar tantance masu neman mafaka da Italiya ta yi da Albania sannan Burtaniya itama ta kulla irin wannan yarjejeniya da Rwanda domin tantance masu neman mafaka.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya tabbatar wa da gwamnonin jihohi cewa gwamnatin za ta ci gaba da nazarin tantance bukatun masu neman mafakar a wata kasa ta daban.
Ya ce zai gabatar da shawarwarinsa a taro na gaba da za a yi tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi a watan Disamba.