Shekaru 30 bayan hadewar Jamus
October 3, 2020Shugabar gwamnatin Jamus da shugaba Frank-Walter Steinmeier na bangaren mahalarta addu'a ta musamman da aka gudanar a majami'ar St. Peter da Paul da ke birnin Potsdam, a bangaren shagulgulan bukin cika shekaru 30 da hadewar yankunan yammaci da gabashin Jamus.
Bukin na Potsdam ya gudana ne a karkashin jagorancin shugaban kasa Steinmeier da wasu mahalarta 230, da ke zama kashi daya daga cikin biyar da aka tsara tun da farko.
Ya ce "A shekara ta 2020, tarayyar Jamus kasa ce da Jamusawa daga yammaci da gabashi, da baki da suka jima da zama a kasar, suka gyara makomarta. Kasa ce da ke alfari da nasarorin da ta samu daga ra'ayoyin da ke da tushe tun a shekara ta 1989, cewar babu wata alaka tsakanin nasarar 'yanci da akasintaIdan muka kalli duniya, da nahiyar Turai, zamu yarda da cewar, abun da muka gada a shekara ta 1989 bai taba zama muhimmi ba kamar a duniyar da muke ciki a yau".
A ranar 3 ga watan Oktoban shekara ta 1990 bangarorin jamus din biyu suka hade a matsayin kasa daya bayan shekaru 40 na yakin cacar baka.
Tsawon wannan lokaci akwai darussa da dama da aka koya a cewar shugaban majalisar tarayyar Jamus Dietmar Woidke: "Zamu iya, kuma ya dace mu yi nazari sosai kan hadin kan Jamus. Koma baya, da rashin nasara da klura kurai na bangaren wannan tafiyar. Sai dai abun la'akari anan shi ne, mun koyi darussa daga garesu".
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tun da farko ta nunar da cewar bukin na bana ba zai yi armashi kamar yadda ya dace ba.
Gabashin Jamus din ta hade da yammaci kasa da shekara guda, matsin lamba na karuwar zanga zanga ya tilasta mahukuntan na gabashi bude katangar da ke raba yankunan biyu, da ake kira "Berlin Wall" da duk sauran shinge da ke tsakaninsu.
" Corona ta koya mana tawali'u. Sauyin yanayi babban klalubale ne ga rayuwarmu. Tsoffin dangantaku na cigaba da lalacewa, duniya na fuskantar koma baya a bangaren tsaro. Yawancin abubuwan da muka rayu da su tsawon shekaru 30 da suka gabata, yanzu babu su".
Saboda annobar COVID 19 din dai bukin na bana bai yi armashi ba, sai dai duk da haka an yi nune nunen tarihin kasar da irin cigaba da ta samu na hade kawuyan yankunanta biyu da suka hade a wuri daya a matsayin kasa daya dukulalliya.
Sai dai a yayin da duk da irin cigaba da aka samu a bangarori daban daban tsawon shekaru 30 da hadewar kasar, har ya zuwa yau yankin gabashi na cigaba da fuskantar koma baya na tattali da wasu lamuran rayuwa, idan aka kwatanta da yankin yammaci.
Sai dai kuma a 'yan shekaru da suka gabata, an daina samun matsalar nan ta kauracewa yankin gabashin da mutane ke yi, maimakon zuwa yankin.