An yi wa 'yan gudun hijira sama da miliyan rijista a Jamus
January 6, 2016Talla
Ministan harkokin cikin gidan Jamus ya kara da cewar sama da 'yan gudun hijira dubu dari hudu ne suka futo daga kasar Siriya da ke kasancewa mafiya yawa.
Ministan harkokin cikin gidan na Jamus Thomas De Maiziere ya fada a ranar Larabar nan cewar kimanin mutane miliyan daya da dubu 91 ne aka yi musu rijista.
A inda ya kara da cewar 'yan Siriya su ne suke da tarin yawa da suka haura dubu 400 yayin da 'yan Afganistan ke da sama da dubu 154 masu biye musu baya su ne 'yan Iraki da suka yi kimamin dubu 122.
Jamus dai a karon farko na kasancewa kasa a tarayyar Turai da ta fi kowace kasa karbar 'yan gudun hijira masu yawa a shekara ta 2015.