1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jumus za ta yi bincike kan harin kasuwar Kirisimeti

December 22, 2024

Masu binciken za su saurari bahasi daga ministar cikin gida Nancy Faeser a ranar 30 ga watan Disamba kan kurakuren da hukumomin kasar suka yi na gaza yin rigakafin harin da aka kai Magdeburg.

https://p.dw.com/p/4oTyZ
Bincike kan harin kasuwar Kirisimeti
Bincike kan harin kasuwar KirisimetiHoto: Sebastian Kahnert/dpa/picture alliance

Gwamnatin Jamus ta yi alkawarin gudanar da bincike domin fayyace kurakuren da hukumomin kasar suka yi na gaza yin rigakafin harin da aka kai kasuwar Kirisimeti ta birnin Magdeburg a ranar Juma'a.

Masu binciken za su saurari bahasi daga ministar cikin gida Nancy Faeser a ranar 30 ga wannan wata na Disamba kan rashin yin katabus daga jami'an tsaro na dakile aukuwar wannan lamari.

Karin bayani: Ana bincike kan barazanar sake kai hari a Jamus

Mujallar Der Spiegel ta ruwaito cewa, shekara guda da ta gabata hukumomin leken asirin Saudiyya sun aike wa takwarorinsu na Jamus gargadi a game da dabi'un maharin, sai dai ba a dauki wani mataki a kansa ba.

Wannan lamari ya birkita lissafi a Jamus tare da janyo matsin lamba ga gwamnatin Olaf Scholz, yayin da ya rage watannin biyu a gudanar da zaben gaba da wa'adi na 'yan majalisun dokoki ta Bundestag.