Dangantaka ta yi tsami tsakanin Jamus da Rasha
September 6, 2020Talla
Dangantaka na kara tsami wanda ta kai Jamus yin barazanar sanya wa Rasha takunkumi, muddin ta ki bada hadin kai a binciken da ake yi.
A wata tattaunawa da ya yi da mujalar Daily Bild, ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ce idan har Kremlin ta ce bata da hannu a cikin wannan lamarin to ta fito da kwararan shaidu domin kare kanta. Maas ya kara da cewa idan kuwa ba su yi haka ba cikin 'yan kwanakin nan da ke tafe to za su dauki matakan da suka dace.
A nata bangare Birtaniya ta ce Rasha na da tambayoyi da za ta amsa. A satin da ya gabata ne Jamus ta sanar da cewar ba makawa Alexei Navalny ya hadiyi gubar sinadarin Novichok mai sarke jijiyoyi.