Jamus za ta sayar wa Saudiyya da makamai
September 20, 2018Talla
Kamfanin dillancin labaran kasar ta Jamus ya ruwaito cewa ministan tattalin arzikin kasar Peter Altmaier a wata wasikar da ya aika wa kwamitin kula da tattalin arziki a majalisar dokokin kasar ya tabbatar da amincewar gwamnatin na sayar wa da kasar ta Saudiyya makamai..
A cikin wasikar minista Altmaier ya bayyana cewa Jamus za ta sayar wa kasar Saudiyya da wasu na'urori hudu na girka makaman atilare. Yarjejeniyar da jam'iyyun da ke kawancen mulki a kasar ta Jamus ta cimma a baya ta tanadi haramta sayar da makamai ga kasar Amirka da kuma Saudiyya kasancewa suna da hannu a yakin kasar Yemen. Sai dai kuma Saudiyya ta kasance babbar aminiyar kasashen yamma a fagyen yaki da Kungiyar IS a kasar Siriya.