Iftila'i: Jamus za ta tura tawaga Lebanon
August 5, 2020Talla
Kawo yanzu fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 100 yayin da dubbai kuma suka jikkata.
Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce lamarin ya lalata mata ofishin jakadancinta na Lebanon. A sakamakon haka tawagar kwararrun ta Jamus za ta je Beirut domin taimaka wa mahukuntan kasar ci gaba da ceto rayukan wadanda lamarin ya shafa.
Wannan na zuwa ne a yayin da Faransa ta sanar da cewa a ranar Alhamis Shugaba Emmanuel Macron zai je Lebanon domin jajanta wa mahukuntan kasar da kuma bayar da taimakon da ya dace.