Jamus:Za ta ci gaba da taimaka wa Afirka
May 3, 2018Talla
Heiko Maas ya ce ko da shi ke hankalinsu ya dauku a game da abin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, amma gwamnatin Jamus ba ta manta ba, da Afirka ba. Minista na harkokin waje na Jamus Heiko Maas ya yi alkawarin cewar Jamus za ta ci gaba da hulda da nahiyar Afirka ta fuskar taimakata a kan sha'anin tsaro da tattalin arziki. Wannan shi ne rangadi na farko da ministan yake yi a wasu kasashen Afirka wadanda suka hada da Habasha da kuma Tanzaniya makwannin shida da ya fara aiki.