An yi jana'izar tsohon shugaban Masar a makabartar talakawa
June 18, 2019Lauyan da ke kare tsohon shugaban kasar ta Masar Mohamed Morsi ya bayyana a yau Talata da cewa an yi jana'aizar Morsin a gaban iyalinsa da dangi da 'yan uwansa na kusa, a wata makabartar talakawa da ke birnin Cairo biyo bayan yi wa gawarsa sutura a babbar asibitin gidan yarin Tora a yammacin jiya Litinin.
Shugaba Mohamed Morsi ya yanke ya fadi ne a jiya a yayin da yake wani jawabin kare kansa a gaban kotun da take tuhumarsa da aikata lekon asiri a Masar, daga bisani kuma ya ce ga garinku bayan an ruga da shi zuwa asibiti.
Dan shekaru 67 a duniya, Mohamed Morsi ya hau kan kujerar mulkin Masar ne karkashin jagorancin babbar jam'iyyar 'yan uwa musulmi ta hanyar zabe, sai dai kafin cika wa'adin shekara daya na mulki sojojin kasar su hambarar da shi a shekarar 2013 biyo bayan zanga-zangar da ta mamaye kasar, wanda tun daga wannan lokacin ya ke fuskantar tuhume-tuhume a gaban kotu.