1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin duniya da dama sun halarci jana'izar Peres

September 30, 2016

Shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas da Firayin Ministan Isra'ila na daga cikin shugabannin da suka halarcin jani'ar tsohon shugaba Shimon Peres wanda ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.

https://p.dw.com/p/2Qm1l
Jerusalem - Benjamin Netanyahu und Mahmoud Abbas bei Beerdigung von Shimon Peres
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Gershom/Handout

Shugabannin duniya da dama sun halarci jana'izar tsohon shugaban Isra'ila Shimon Peres da aka gudanar a wannan Jumma'ar, inda suka yabi irin rawar da ya taka a rayuwarsa. Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana Peres a matsayin daya daga cikin gwarzayen al'umma. Idan za'a iya tunawa dai, marigayi Shimon Peres ya yi ta gaggwarmaya don ganin cewar an samar da zaman lafiya tsakanin Ira'ila da Falesdinawa.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba yana da shekara 93 a duniya.Daga cikin wadanda suka halarci jana'izarsa har da shugaban Jamus Joachim Gauck, da shugaban Amirka Barack Obma da Yerima Charles mai jira gado a masara'autar Birtaniya. Daidai da shugabannin Falesdinawa Mahmud Abbas ma ya halarci jani'ar, duk da cewa tattaunar wanzar da zaman kafiya tsakanin Isra'ila da Falesdinawa ta tsaya cik tun shekaru biyun da suka gabata.