Jaridun Jamus: 06.12.2024
December 6, 2024Da farko sharhin jaridar Süddeutsche Zeitung ya mayar da hankali kan sauyin shugabanci da aka samu a kasar Namibiya inda aka karon farko mace ta lashe zaben shugabancin kasa. Jaridar ta ce nasarar da Netumbo Nandi-Ndaitwah ta samu ya haifar da kyakkyawan fata a fuskar samar da daidaito a wannan kasa ta Afirka. Ellen Johnson Sirleaf ta kasar Laberiya ce ta kasance mace ta farko da ta yi nasara a zaben shugaban kasa a nahiyar Afirka, inda ta yi wa'adi biyu. Amma a yanzu Samiya Suluhu Hassan ta hau kujerar mulkin Tanzaniya a 2021bayan mutuwar shugaba mai ci. Saboda haka Netumbo Nandi-Ndaitwah da ake wa lakabi da NNN ta zama mace shugabar kasa ta uku a nahiyar.
Süddeutsche Zeitung ta ci gaba da cewa, ba wai kawai kasancewar ta mace ce abin yabawa, a'a, amma Netumbo Nandi-Ndaitwah mai shekaru 72 da haihuwa ta samu kashi 58% na kuri'un da aka kada, lamarin da ya zama sakamako mafi kyau da jam'iyyarta ta Swapo da ke mulki ta taba samu. Jaridar ta ce wannan ya nuna irin bijire wa guguwar sauyi da ke kadawa a Afirka da Namibiya ta yi, inda jam'iyyun da ke mulki a Afirka suke samun rashin nasara a zabuka. Amma duk da cewa Netumbo Nandi-Ndaitwah na matukar mutunta al'adu da addinan al'ummar Namibiya, amma kuma fafutukar kare hakkokin mata sun taka rawa sosai a yakin neman zabenta. Dama jam'iyyarta ta Swapo ta yi ruwa da tsaki wajen kara kason mata a majalisa inda ya tashi daga kashi 8% a 1990 zuwa kashi 50%
A nata bangaren, Berliner Zeitung ta yi sharhi ne kan ziyarar da ministan tattalin arzikin Jamus Robert Habeck ya kai Kenya a farkon mako, inda ya yaba ta a matsayin kasa abar koyi a fannin makamashi da ke sabuntawa da kuma tattalin arziki. Jaridar ta babban birnin tarraya ta ce wannan ita ce ziyara ta karshe da Habeck ya yi a kasar waje kafin zaben da zai iya kawo karshen gwamnatinsu ta hadin gwiwa, amma dai kasar ta gabashin Afirka ta burge shi saboda manufofinta sun yi daya da na kasashen Turai a fannin makamashi. Berliner Zeitung ta ce Kenya na samar da kashi 90% na bukatunta na wutar lantarki daga makamashin da ake iya sabuntawa. Saboda haka, Habeck ba wai kawai yana ganin Kenya a matsayin ja gaba ba, amma kuma yana daukan ta a matsayin abokiyar tafiya a wannan fanni. Gwamnatin Kenya na da burin samun wadatar makamashi kan nan da 2030, lamarin da ya sa ministan tattalin arzikin Jamus Robert Habeck ke neman hadin gwiwa don kasarsa ta ci gajiya.
Ita kuwa jaridar die Tageszeitung ta yi nazari ne kan ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden ya kai kasar Angola, inda ta kwatanta wannan ran gadi da hanyar samar da zaman lafiya na Biden saboda Angola ce ke shiga tsakani tsakanin rikicin da ke hada Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango da Ruwanda. Jaridar ta ce a daidai lokacin Joe Biden ya isa Angola domin gudanar da ziyararsa ta farko kuma ta karshe a Afirka, rikici ya sake ta'azzara a gabashin Goma na Kwango a tsakanin sojojin gwamnatin kasar da 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda. Die tageszeitung ta ce karuwar tashin hankali a ziyarar Biden a Angola ba abin mamaki ba ne, domin matsin lambar Amurka ne ya taimaka a farkon watan Agusta wajen cimma tsagaita wuta bisa shiga tsakani na shugaban Angola João Lourenco a madadin Kungiyar Tarayyar Afirka. Saboda haka, Biden ya zo yaba rawar da Angola ke takawa a fannin warware rikcice-rikice da kuma karfafa manufofin tsaro da ke tsakaninsu.
Ita kuwa jaridar Zeit Online ta raja'a ne kan fannin kiwon lafiya a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, inda watanni kalilan bayan barkewar kyandar biri, wata sabuwar cutar da aka kasa gane kanta ta yi sanadin mutuwar mutane da dama. Jaridar ta ce fiye da mutane 60 sun mutu bayan barkewar wata cutar da ke kama da mura da ta fi shafar yara 'yan kasa da shekaru 15 da haihuwa a yankin kudu maso yammacin kasar. Ministan lafiya Apollinaire Yumba ya ce duk wadanda suka mutu sun fara kamuwa da zazzabi da matsalar numfashi da kuma karancin jini. A yanzu dai mutane 376 ne wadannan alamomi na rashin lafiya suka shafa a yankin Panzi na Kwango. Zeit Online ta ruwaito cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ba ta yi sako-sako da wannan cuta da ta bulla a Kwangon, inda ta tura da tawagar kwararru domin su yi aiki kafada da kafada da masana cututtuka na wannan kasa.