1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Barazanar yunwa a wasu sassa na Afirka

Mohammad Nasiru Awal
February 24, 2017

Barazanar matsalar yunwa da wasu kasashen Afirka ke fuskanta ta mamaye labaran jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka wannan makon.

https://p.dw.com/p/2YCAs
Hoton Yunwa a Nijeriya
Ana fama da yunwa a wasu kasashen Afirika.Hoto: picture-alliance/dpa/Unicef/NOTIMEX

A tsokacin da ta yi kan batun jaridar Der Tagesspiegel ta fara ne da cewa a karon farko tun a shekarar 2011, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da aukuwar wani bala'i na matsananciyar yunwa a wasu kasashe hudu ciki har da guda uku na Afirka da suka hada da Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma Najeriya. Dalili kuwa shi ne mummunan farin da ya addabi gabacin Afirka, sannan a Somaliya da arewacin Kenya da kuma kasar Habasha ana samun labarai makamantan wannan. Yakin basasar da ake yi a Sudan ta Kudu tun shekarar 2013 ya jefa kasar cikin halin rashin abinci ga al'ummarta. Yayin da rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya shi ma ke zama sanadin samun matsalar matsananciyar yunwa a yankin. Jaridar ta ce idan aka dubi lamarin da idon basira za a ga cewa dukkan yankunan da ake magana kansu na yiwuwar fuskantar matsalar yunwa, suna fama da yake-yake.

Shugaba Mugabe tsohon mai ran karfe

Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban da ya fi tsawon shekaru a AfirkaHoto: picture alliance/AP Photo/T.Mukwazhi

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a wannan makon ta leka kasar Zimbabuwe musamman ma shugaban mulkin karya na kasar wato Robert Mugabe da a wannan makon ya cika shekaru 93 a duniya amma yana ci gaba da rike madafun iko.

Ta ce rayuka da yawa na Robert Mugabe wanda saboda farin jininshi a wajen 'yan kasar, matarsa wato Grace Mugabe ta ce ko gawarsa za ta tsaya takara tana da kyakkyawar damar yin nasara fiye da sauran 'yan takara. Mugabe da ke rike da shugabancin kasar tun lokacin samun 'yancin kai a 1980 ya sha alwashin tsayawa takara a zaben shugaban kasa da zai gudana cikin shekaru biyu masu zuwa. Jaridar ta ce Mugabe wanda a shekarun baya ya taka rawar gani a ci gaban kasar, tuni ya bata rawarsa da tsalle, ya kuma mayar da kanshi wani abin dariya.

Ci da gumin manoman koko na Afirka

Ghana Kakao-Anbau
Farashin koko ya fadi a kasuwannin duniyaHoto: picture-alliance/robertharding

Koko na da arha amma cokulat na da tsada inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai cewa yayin da farashin danyen koko a kasuwar duniya ya fadi kasa, masu amfani da kaya ba su gani a kasa ba, domin farashin cokulat wanda da koko din ne ake sarrafa shi yana kara hauhawa.

Jaridar kamanin kashi 70 cikin 100 na koko da ake samarwa a duniya na fitowa ne daga yankin yammacin Afirka a duk lokacin da kaka ta yi gardama farashinsa na tashi, amma da zarar kaka ta yi kyau sai farashinsa ya fadi, lamarin da ke shafar rayuwar kananan manoma a Afirka ta Yamma wadanda ba sa ganin wani sauyi na irin hada-hadar da ake yi da wannan haja a kasuwar duniya, musamman wadda ta shafi cokulat. Yanzu haka dai wasu manyan kungiyoyin kwadago da ke wakiltar manoman koko kimanin dubu 100 a kasar Cote d'Ivoire sun yi barazanar shiga yajin aiki da fatan matakin zai yi tasiri a kan farashin koko a duniya.