1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Fatan samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu

Mohammad Nasiru AwalApril 29, 2016

Komawar Riek Machar birnin Juba na zama wani kwakkwaran matakin farko na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/1IfW9
Südsudan Juba Inaugurierung Rebellenführer Riek Machar
Hoto: Getty Images/AFP/S. Bol

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus da jaridar Die Tageszeitung wadda ta ce haulolin yaki sun koma matakin farko tana mai nuni da komawar madugun 'yan adawar kasar Sudan ta Kudu Riek Machar kan mukaminsa na mataimakin shugaban kasa abin da ta ce a hukumance ya kawo karshen yakin basasan kasar, amma ta ce bai kawo karshen tashe-tashen hankula da gwagwarmayar neman rike madafun iko a birnin Juba ba. Ta ce dubban mutane ne suka mutu sannan fiye da miliyan biyu suka tsere daga kasar tun bayan barkewar yakin basasa a karshen shekarar 2013. Bikin komawar Machar birnin Juba na zama wani kwakkwaran matakin farko na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

Fata kadan na samun zaman lafiya

Ita ma a sharhin da ta yi kan kasar ta Sudan ta Kudu jaridar Berliner Zeitung ta ce madugun 'yan tawaye Riek Machar ya koma birnin Juba amma Shugaba Salva Kiir ba ya tunanin sauyin gwammati. Jaridar ta cigaba da cewa duk da aiwatar da wannan bangare na yarjejeniyar zaman lafiya, abubuwan da ke faruwa a kasa ba sa karfafa guiwar yin babban fatan cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali za su wanzu a kasar mai fama da matsaloli iri dabam-dabam.

Rashin shugabanci na gari a Afirka

A wannan makon jaridar Süddeutsche Zeitung labari ta buga game da shugabannin kasashen Afirka da a shekarun baya ake wa kallon wadanda za su daidaita al'amura a nahiyar amma yanzu suka rikide suka zama shugabannin kama karya.

AU Gipfel in Addis Ababa 2013
Wasu daga cikin shugabannin Afirka na yanzuHoto: Getachew Tedla HG

Ta ce a wata nahiya da ta kasa bacewa daga kanun labaru marasa dadi, akwai bukatar samun gwarzaye cikin gaggawa da za su magance matsalolinta. A cikin shekaru gomman da suka wuce irin wadannan mutane sun bayyana amma kuma sun bace a Afirka. Shin me ya faru da su ne? Jaridar ta ba da misali da sabon shugaban kasar Tanzaniya wanda tun bayan darewarsa kan mulki a watan Nuwamban 2015 yake yaki da cin hanci da rashawa, ya rage yawan wakilan majalisar ministoci yana kuma aiwatar da aikace-aikacen raya kasa, abin da ya jawo masa farin jini tsakanin al'umma. Sai dai ire-irensa ba sa dadewa kan mulki ba. Cikinsu kuwa akwai Patrice Lumumba na Kwango da Thomas Sankara na Burkina Faso, da aka katse musu hanzari. Sai dai wasunsu irinsu Yoweri Museveni na Yuganda da Robert Mugabe na Zimbabuwe da a farkon kama ragamar shugabanci suka yi abin a zo a gani amma daga baya sun zama 'yan kama karya.

Lambar yabo kan rahoton ta'sar Boko Haram

A yammacin ranar Alhamis a birnin Hamburg mujallar Die Zeit ta yi bikin mika kyautar Nannen da ke zama mafi shahara ga kyaututtukan da ake ba wa 'yan jarida a Jamus. A bana dan jarida na mujallar ta Die Zeit, Wolfgang Bauer ya ci kyautar dangane da bayanai da ya tattara a cikin wani rahoto game da ta'asar da kungiyar Boko Haram ta yi musamman a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Shi dai dan jaridar ya yi hira da 'yan mata da kuma matan da Boko Haram ta taba yin garkuwa da su, amma suka kubuta.

Bankwana da mawakin zamani na Afirka

Demokratische Republik Kongo Papa Wemba ist gestorben
Hoto: Getty Images/AFP/J.-D. Kannah

Mu kammala da mutuwar shahararren mawakin nan dan kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango Papa Wemba, da Allah Ya yi wa rasuwa a karshen mako lokacin wasan kida a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire, wanda jaridar Der Tagesspiegel ta kwatanta shi da tauraro a fagen kide-kide da wake-wake na duniya, sannan a Afirka yana zaman mawakin zamani. Jaridar ta ce ba masoyansa kadai ne suka yi wannan rashi ba, mambarin wasan kida ya rasa wani gurbi da zai wahala a cike shi nan gaba kadan.