Gasar AFCON ta dauki hankali a Jamus
January 7, 2022Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhinta mai taken: Firaminista Abdalla Hamdok ya yasar da kwallon mangwaro ya huta da kuda, a yanzu gwamnatin soja a Khartum ta rasa bangaren farar hula. Jaridar ta ci gaba da cewa ba alamar Sudan za ta samu lafawar al'amura, inda masu zanga-zanga suka ci gaba da yin bore a manyan biranen kasar na Khartoum da Omdurman. Firaminista Abdullah Hamdok ya yanke shawarar barin mulki, watanni uku bayan da sojoji suka mayar da shi kan karagar mulkin da suka kore shi a kai tare da yi masa daurin talala. Ita kuwa jaridatar die Tageszeitung, ta yi nata sharhin ne kan hari da aka kai a Jamhuriyar Benin a wani wurin shakatawa da ke kusa da kan iyakarta da Togo da Burkina Faso a watan Disambar bara. Harin da sojoji suka dora alhakinsa a kan masu ikirarin jihadi, ya halaka sojojin biyu. A baya dai, Benin ba ta taba fuskantar irin wannan hari ba.
Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung, ta rubuta nata sharhin ne kan sabon nau'in corona. Jaridar ta ce yanzu kam an fara sassauta dokokin corona a kasar Afirka ta Kudu, bayan da a a watan Nuwambar bara labarin aka samu bulllar sabon nau'in corona da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana da nau'in Omicron. Matafiya daga Afirka ta Kudu sun ga ta kansu a fadin duniya, inda aka sanya musu takunkumin hana shiga kasashe da dama. Matakin dai ya shafi tattalin arzikin kasar. da ma dai Afirka ta Kuudun, na zaman tamkar wata cibiya ko makyankyasar coronavirus a Afirka ta Kudu tun bayan da annobar ta bulla a duniya.
Jaridar Süddeutscher Zeitung kuwa ta yi sharhinta ne kan gasar cin kofin Afirka, inda ta ce kaptin din kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang ya kamu da corona, kwanaki kalilan gabanin gasar. Kamuwar fitaccen dan wasan Aubameyang ya sanya bayyana bukatar daukar tsauraran matakan da suka dace a yayin gasar ta cin kofin nahiyar Afirka AFCON, domin gudun yaduwar annobar coronan da ta adddabi duniya baki daya.