1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Karshen Ebola a Yammacin Afirka?

Mohammad Nasiru AwalJanuary 15, 2016

Ayyana kawo karshen cutar Ebola a Laberiya da girke karin sojojin Jamus a Mali da sabon tashin hankali a Darfur sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1HeJa
Liberia WHO erklärt Westafrika für Ebola-frei
Hoto: Reuters/J. Giahyue

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus ne da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta duba annobar cutar Ebola a yammacin Afirka.

Ta ce a hukumance a ranar Alhamis aka ayyanar karshen cutar Ebola a kasar Laberiya, abin da ya kawo karshen annobar cutar a yankin Yammacin Afirka, inda aka samu bullar cutar mai saurin kisa a shekarar 2014. To sai dai masu bincike kan kwayoyin cutar sun ja hankali da a koyi darussa na hakika daga cutar da ta hallaka dubbban mutane a kasashen Laberiya, Guinea da Saliyo.

Sojojin Jamus a yankin mai hatsari na Mali

Har yanzu dai muna a yankin na Yammacin Afirka. A labarin da ta buga mai taken "Kayan aiki na musamman ga sojojin rundunar Jamus ta Bundeswehr a Mali", jaridar Bild cewa ta yi:

Bundeswehr in Mali EU-Ausbildungsmission
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

Aikin da sojojin Jamus za su yi a Mali karkashin tutar Majalisar Dinkin Duniya yana da hatsari fiye da yadda aka yi tsammani. Jaridar ta rawaito wasu rahotanni na Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa a cikin watanni ukun karshe na shekarar 2015, an kai hare-hare har 28 a kan tawagogin majalisar, inda aka kashe sojojinta guda biyu. A saboda haka rundunar Bundeswehr za ta je da ofisoshi da dakunan kwana na tafi da gidanka na musamman, wadanda rokoki da gurnati ba sa iya hudawa. Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta fada wa jaridar ta Bild cewa yankin Gao da za a girke sojojin kasar yana da hatsari shi yasa za a yi musu tanadin kariya ta musamman.

Sabon tashin hankali a lardin yammacin Darfur

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Sudan tana mai cewa, an murkushe wata zanga-zanga da karfin tuwo sannan sai ta ci gaba kamar:

Sudan Darfur UN Mission UNAMID
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Gonzales

A wani sabon tashin hankali a yankin Darfur da ke yammacin Sudan ya janyo hankalin duniya game da wani yaki da aka manta da shi. Hukumomi sun ce mutane shida sun mutu amma ratohanni daga yankin sun ce yawansu ya fi mutum 13 lokacin da dakarun gwamnati suka bude wuta kan 'yan gudun hijira da ke zanga-zanga a birnin El-Geneina shalkwatar lardin Darfur ta Yamma. Rahotanni sun yi nuni da cewa a ranar Lahadi 'yan gudun hijirar sun mamaye ginin gwamnati a birnin sannan suka yi wani bore a kan titi. An tarwatsa su da karfin tuwo inda aka halaka mutane shida. A ranar Litinin lokacin da ake shirin yi musu jana'iza sojoji sun sake bude wuta inda suka kashe karin mutane uku. Su dai 'yan gudun hijirar sun yi kaura ne daga kauyen Mouli inda a ranar Jumma'a aka yi mummunan bata kashi tsakanin kauyawan da sojoji sa-kai magoya bayan gwamnati.

Karin giwayen Zimbabwe ga China

Shirye-shiryen gwamnatin Zimbabwe na sayar wa kasar Sin wato China karin giwaye da sauran namun dawa na shan suka da kakkausan lafazi daga kungiyoyin kare hakin dabbobi, har wayau dai inji jaridar Die Tageszeitung. Kungiyar kare muhalli ta kasar wato "Zimbabwe Conservative Task Force" ta ce ana cin zarafin giwaye ya zama ruwan dare a China. Gwamnatin Zimbabwe dai ta ce sayar da giwayen yana da muhimmanci domin tana bukatar kudin ceto gandun dajinta da ke fama da kamfar ruwa da mafarauta da ke kashe namun dajin ba bisa ka'ida ba.