Jaridun Jamus: Kerry a Najeriya da rikicin Sudan ta Kudu
August 26, 2016Bari mu fara sharhin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta fara da cewa Kerry ya yaba da kokarin sojojin Najeriya sannan sai ta ci-gaba da cewa.
A farkon mako kakakin rundunar sojojin Najeriya ya ce an yi wa jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau mummunan rauni a kafadarsa a wani harin da sojojin kasar suka kai kan sansanin 'yan bindigar da ke a dajin Sambisa, inda kuma aka halaka mayakan Boko Haram kimanin 300. Ba bu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labari. Ko da ma dai sau biyar rundunar sojin Najeriya ke cewa ta kashe Shekau. Jaridar ta ce wannan labarin nasarar da sojin Najeriya suka samu ya zo ne a ranar da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerrya ya fara wata ziyara da ke zama irinta ta uku cikin shekaru biyu a Najeriya. A jawabin da ya yi a garin Sakkwato Kerry ya yaba da yakin da sojojin Najeriya ke yi da Boko Haram da kuma irin nasarorin da suka samu a watannin bayan nan. Ya kuma yaba da canje-canje da ake yi cikin rundunar kasar, inda ya yi kira da a kiyaye hakin dan Adam.
Babban koma baya ga jam'iyyar ANC
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon ta leka kasar Afirka ta Kudu tana mai cewa jam'iyyar ANC ta rasa birnin Johannesburg.
Jaridar ta ce a karon farko tun bayan kawo karshen mulkin wariya a 1994 'yan adawa za su tafiyar da harkokin mulki a Johannesburg, birni mafi girma a Afirka ta Kudu. Ta ce wannan babban koma baya ne ga jam'iyyar ANC da ke jan ragamar mulkin kasar. Hukumar gudanawar birnin ta zabi dan takarar jam'iyyar Democratic Alliance, DA a takaice, Herman Mashaba mai shekaru 56 a matsayin sabon magajin garin birnin. Da ma dai masharhanta sun kwatanta zaben kananan hukumomin da ya gudana a fadin kasar a kwanakin baya da wani zakaran gwajin dafi ga jam'iyyar ANC a zhaben shekarar 2019 wanda bisa dokar kasa Shugaba Jacob Zuma ba zai iya tsayawa takara ba.
Riek Machar ya samu mafaka a Sudan
Sudan ta tabbatar da karbar tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar wanda ya tsere daga birnin Juba inji jaridar Die Tageszeitung.
Ta ce an sake shiga rudu a kokarin neman zaman lafiya a Sudan ta Kudu. Riek Machar wanda rikici tsakaninshi da Shugaba Salva Kiir da ya jefa Sudan ta Kudu cikin yakin basasa, ya samu mafaka a Khartoum babban birnin makwabciyar kasa Sudan, wadda a 2011 Sudan ta Kudu din ta balle daga gareta. Sai dai wata sanarwar gwamnatin birnin Khartoum ta ce Machar yana kasar ne don jinya kuma da zarar ya samu sauki zai zarce kasar da yake son tafiya. Jaridar ta ce ba wa Machar mafaka zai ba wa gwamnatin Sudan din wani makamin samun angizo a yakin basasar Sudan ta Kudu.