1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Museveni da mulkin sai Mahdi ka ture

Mohammad Nasiru AwalFebruary 19, 2016

Zaben shugaban kasa a Yuganda da yajin aikin gama gari a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da batun tsaro a Afirka sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

https://p.dw.com/p/1HyXA
Yoweri Museveni Präsident Uganda
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Hoshiko

Za mu fara sharhunan jaridun na Jamus kan nahiyar Afirka ne da jaridar Der Tagesspiegel wanda ta yi tsokaci kan zaben shugaban kasar Yuganda tana mai cewa tun ba a gudanar da zaben ba an san wanda zai yi nasara sannan sai ta ci gaba kamar haka.

"A karo na biyar shugaban kasa Yoweri Museveni dan shekaru 71 wanda kuma ya kwashe shekaru 30 kan karagar mulki, shi zai lashe zaben na ranar Alhamis. Amma abin mamaki duk da haka dukkan 'yan takara sun dauki yakin neman zaben da muhimmanci, musamman kasancewa a wannan karon ba sanannen abokin adawar nan wato Kizza Besigye kadai ne Museveni ya fuskanta ba, akwai na biyunsu wato tsohon Firaminista kuma tsohon na hannun damar Museveni tsawon shekaru, Amama Mbbabazi wanda ya yi takara a matsayin indipenda.

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta buga labari kan zaben na Yuganda tana mai cewa Yoweri Museveni ya kuduri aniyar darewa kan kujerar mulkin kasar har sai bayan ransa. Ta ce shekaru 30 da suka wuce lokacin Museveni ya zama wani dan siyasa da aka dora babban fata kansa. Yanzu ya kankane dukkan lamura a kasar da ke yankin gabashin Afirka, su kuma 'yan adawa ba su da wani katabus.

Yajin aikin gama gari ya gurgunta harkokin yau da kullum

Kongo Vital Kamerhe Oppositionsführer
Yajin aikin da 'yan adawar suka kira ya samu karbuwaHoto: Getty Images/AFP/F. Scoppa

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ne tana mai nuni da yadda harkoki suka tsaya cak sakamakon wani yajin aikin gama gari da 'yan adawa suka kira don nuna fushi ga dage ranar zabe a kasar.

Ta ce yajin aikin na gama gari da 'yan adawar suka kira a ranar Talata don yin tir da dage zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga watan Nuwamban, ya samu karbuwa, inda masu fafatukar suka ce kasuwanni da shaguna da ofisoshi da sauran hada-hadar yau da kullum sun tsaya cak. Yajin aikin dai ya tafi salin-alim in ban da a wasu biranen inda da sanyin safiyar ranar ta Talata aka kame wasu jagororin 'yan adawa.

Shugabannin Afirka wani bangare ne na matsalar nahiyar

Kenia Gedenken in Eldoret - Uhuru Kenyatta & Muhammadu Buhari
Daga dama: Uhuru Kenyatta, Muhammadu Buhari da Hassan Sheik MohamudHoto: Reuters/T. Mukoya

A karshe sai jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta ce kungiyoyin 'yan tarzoma sun addabi nahiyar Afirka, yayin da dubun dubatan 'yan nahiyar ke tserewa daga mulkin danniya da talauci. Sai dai shugabannin Afirka na gabatar da kansu a matsayin masu tabbatar da tsaro duk da cewa su din ma wani bangare ne na wannan matsala.

Jaridar ta yi nuni da babban taro kan tsaro da ya gudana a birnin Munich a karshen makon jiya inda ta ce a karon farko an gaba da wani shiri musamman don kasashen Afirka, inda wakilai daga nahiyar suka yi magana kan sha'anin tsaro da ya shafi muradun kasashen yamma, wato tarzoma ta addini da kuma gudun hijira. Sai dai jaridar ta ce sakon da manyan kasashen Afirka a gun taron suka bayar na nuna cewa kwanciyar hankali da tsaro sun gabaci mulki da doka da kuma kare 'yancin dan Adam. Kuma abin takaici ba wanda ya kushe wannan matsayin na shugabannin Afirka.