1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Rigingimu a wasu lardunan kasar Yuganda

Mohammad Nasiru AwalApril 1, 2016

Tashin hankali a yammacin Yuganda tun bayan zaben kasar da rikicin siyasa a Zanziba sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1IO4L
Uganda Kampala Wahlen Ausschreitungen Proteste
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Za mu fara sharhin da jaridar Die Tageszeitung wadda a wannan makon ta leka kasar Yuganda tana mai cewa adduna da sojojin sa kai maimakon giwaye da 'yan yawon bude ido.

Ta ce tun bayan zaben kasar Yuganda da ake takaddama kai, ake fama da tashin-tashina a yammacin kasar, inda a da aka saba ganin hada-hadar 'yan yawon bude ido, yanzu yankin ya zama tamkar fagen daga. Tun bayan zaben watan Fabrairu yammacin kasar ta Yuganda musamman ma a kusa da tsaunin Rwenzori, ya zama wurin aikata kisan gilla. A makonni da suka gabata an kashe akalla mutane 30 a lardunan Bundibugyo da Kasese daukaci an yi musu gunduwa-gunduwa da adduna. An kuma kone gidaje fiye da 360. Mutane da yawa sun tsere daga yankin. Saboda muni lamirin a ranar Talata shugaba Yoweri Museveni ya kai ziyarar gane wa ido a yankin. Har yanzu dai ba a gano wadanda suka aikata wannan kisan gilla ba.

Dambarwar siyasa a tsibirin Zanziba

An samu wanda ya yi nasara a zaben majalisar dokokin da aka sake gudanarwa a tsibirin Zanziba na kasar Tanzaniya, amma duk da haka ba a warware rikicin gwamnati ba, abin da ya sanya damuwa ga mahukuntan birnin Dares Salam inji jaridar Neues Deutschland.

Tansania Sansibar Wahlen Wiederholung Präsident Ali Mohamed Shein
Ali Mohamed Shein na jam'iyyar CCMHoto: Reuters/E. Herman

Ta ce mutumin da ya lashe zaben Zanziba na cikin tsaka mai wuya. Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, dole Ali Mohamed Shein na jam'iyyar CCM ya kafa gwamnatin hadaka a tsibirin, da za ta samu wakilcin 'yan adawa matukar sun samu akalla kashi 10 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada. To sai dai babbar jam'iyyar adawa ta CUF ta kaurace wa zagaye na biyu na zaben ranar 20 ga watan Maris, bayan an soke sakamakon wanda aka gudanar cikin watan Oktoban bara wanda CUF din ta yi ikirarin lashewa. Babu dai wata jam'iyyar adawa da ta samu kashi 10 cikin 100 da ake bukata. Duk da tattaunawar neman mafita da ta gudana tsakanin bangarorin biyu wato CCM da CUF har yanzu da sauran rina a kaba musamman a dangane da warware rikicin da gwamnatin tsibirin ta fada ciki.

Tasirin agaji don kyautata makomar yara

Ilimi gishirin zaman duniya
Hoto: DW/H. Fischer

Tallafi daga birnin Bonn zuwa ga yara a kasar Burkina Faso inji jaridar Genaral-Anzeiger tana mai mayar da hankali kan wasu aiyukan tallafa wa yara a kasar ta Burkina Faso da wata kungiya mai suna "Ba wa yara makoma" ke yi. Ta ce ba da dadewa ba ne shugabar kungiyar kuma likita 'yar asalin Bonn Maria Radioff ta dawo daga kasar ta Burkina Faso, inda baya ga sa ido a kan aiyukan da kungiyar ke yi, ta kuma ba da tallafi na kiwon lafiya ga yara marasa galihu da ke zaune a unguwannin da ke wajen birnin Ouagadougou. Jaridar ta rawaito likitar na cewa ta gano sabbin abubuwa da ke nuni da muhimmancin yadda kananan aiyukan taimakon ke yin babban tasiri mai ma'ana a rayuwar al'umma.