1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afirka a Jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal LMJ
December 28, 2018

Zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da zanga-zangar Sudan sun dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3Ak2A
Kongo Beni | Protest & Demonstration gegen Ausschluss von Wahl
Dage zabe a Kwango ya bar baya da kuraHoto: Reuters/S. Mambo

A sharhinta jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta nunar da cewa al'ummar Kwango mutum miliyan 1.25 ba za su kada kuri'a a zabe ba. Ta ce zaben da aka shirya gudanarwa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na ranar 23 ga watan Disamba na kara zama wani abin al'ajabi, domin ba ya ga dage gudanar da zaben da mako guda wato zuwa ranar 30 ga watan na Disamba, hukumar zaben kasar wato CENI ta ce ba za a iya gudanar da zabe a wasu gundumomi ba saboda cutar Ebola da rikici na masu tada zaune tsaye. Hukumar ta ce a watan Maris na shekarar 2019, za a gudanar da zabukan a wadannan gundumomi. Kamata ya yi dai a rantsar da sabon shugaban kasa a ranar 18 ga watan Janairu mai kamawa.

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi tsokaci kan zaben na Kwango inda ta ce an takaita zabe yayin da fada ke kara yawa. Ta ce tun ba yau ba wa'adin mulkin shugaban kasa Joseph Kabila ya kare, amma shugaban na ci gaba da mulki a kasar. A karshen mako za a gudanar da zaben shugaban kasa da zai maye gurbin Kabila, amma hukumar zabe ta ce ba za ai zaben a wasu yankuna ba saboda cutar Ebola da kuma tashe-tashen hankula. Da ma dai ana saka ayar tambaya ko hukumar ta CENI za ta shirya zaben cikin gaskiya da adalci.

Al'umar kasar Sudan sun kuduri aniyar kifar da gwamnati inji jaridar Die Tageszeitung. Ta ce zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa ta rikide ta kuma yadu zuwa wani boren adawa da gwamnatin Shugaba Omar Hassan al-Bashir. Jaridar ta ce zanga-zanga da yajin aiki sun kassara harkokin yau da kullum a Sudan. Zanga-zangar da ta faro  daga adawa da karin farashin burodi da man fetur, cikin sauri ta zama zanga-zanga ta neman Shugaba Omar al-Bashir da ya kwashe shekaru 29 kan mulki ya yi murabus. A Sudan ana yawaita samun zanga-zanga ta adawa da matsin tattalin arziki da halin kunci na rayuwa, amma a wannan karon lamarin ya yi muni. 'Yan sanda da sojoji sun yi amfani da karfin tuwo a kokarin murkushe zanga-zangar, abin da ya yi sanadi na rayuka da yawa.

A karshe sai jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta leka kasar Ethiopia wato Habasha tana mai cewa rigingimu na kabilanci na karuwa a Habasha, abin da ke sanya shakku ko Firaminista Abiy Ahmed zai yi nasara a kokarin shimfida sahihiyar dimukuradiyya a kasar da ke yankin Kahon Afirka. A Addis Ababa babban birnin kasar dai komai na tafiya yadda ya kamata, sai dai a can yankunan karkara ba haka lamarin yake ba, domin rikice-rikice da tilasta wa mutane tserewa daga yankunansu sun zama ruwan dare.