1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Taron sauyin yanyin Afirka a jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala LMJ
September 8, 2023

Taron sauyin yanayi na Afirka na farko da kuma yawan juyin mulki a kasashen Afirka rainon Faransa, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/4W7a5
Afirka | Sauyin Yanayi | taro | Kenya
Kasashen Afirka na son daga muryarsu kan batun sauyin yanyi a duniyaHoto: Khalil Senosi/AP/picture alliance

Jaridar Die tageszeitung ta ce damarmaki ga taron koli kan sauyin yanayi, shugabannin Afirka sun daga murya gabanin babban taron sauyin yanayi na duniya domin samun sauyi zuwa makamashi mara gurbata yanayi sai dai kasashe masu ci-gaban masana'antu ya kamata su cika alkawari. Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce kashi hudu cikin 100 na hayakin masana'antu ne kacal kasashen Afirka suke fitarwa. Kasashe da dama na nahiyar suna son magance matsalalolin sauyin yanayi, sai dai suna bukatar taimako.

Karin Bayani: Sauyin yanayi da tsattsauran ra'ayi a Sahel

Süddeutsche Zeitung ta ce gudummawar Afirka ga dumamar duniya ba ta taka kara ta karya ba amma kuma ita ce ta fi jin radadin abin, a dangane da haka a yanzu tana son zama ja gaba wajen sauyin dabarun makamasi mai tsafta. Dukkan jaridun dai sun yi itifakin cewa taron sauyin yanayin na Afirka na son aike wa da sako cewa kasashen Afirka suna bukatar taka muhimmiyar rawa a muhawarar sauyin yanayi ta duniya ba kawai a matsayin nahiyar da ke shan wahalar dumamar duniya ba, amma a matsayin wacce za ta bayar da gagarumar gudunmawa da kuma ke da damarmaki na kawo sauyin makamashi mai tsafta mara gurbata muhalli.

Njar | Yamai | Juyin Mulki | Kin Jinin Faransa
Kasashe rainon Faransa na fuskantar juyin mulki da nuna kin jinin uwar gijiyar tasuHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Jaridar Neuer Zürcher Zeitung da Frankfurter Allgemeine Zeitung sun yi tsokaci kan juyin mulki a Afrika tare da tambayar shin me yake faruwa da Afirka?. Juyin mulki tara cikin shekaru uku, suka ce juyin mulki ya dawo a Afirka da dalilai mabambanta. A watan Yuli an yi juyin mulki a Nijar, bayan 'yan makonni kuma aka yi a Gabon. Yayin da a Nijar sojoji suka yi togaciya da rashin tsaro wajen juyin mulki, a Gabon kawar da mulkin kaka-gida ne na iyalan Ali Bongo. Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce bayan ja-in ja da kai ruwa rana, Faransa za ta janye wasu sojojinta daga NIjar ta mayar da su Chadi.

Karin Bayani: Ecowas za ta yaki sojojin Nijar

Jaridar ta  ce a yanzu Faransa na tattauna janye sojojin salin alin daga NIjar, a cewar ma'aikatar tsaron kasar a birnin Paris. Sai dai kuma a waje guda tana ci gaba da jaddada cewa gwamnatin mulkin sojin haramtacciya ce, tana nan a kan bakarta na dawo da hambararren shugaban da aka zaba na dimukuradiyya Bazoum Mohammed kan karagar mulki. A nasu bangaren jagororin mulkin sojin, tun a watan Augusta suka sanar da soke yarjejeniyar huldar soja da Faransa suke kuma bukatar Faransan ta janye daukacin sojojinta 1,500 da ke kasar.