1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: 'Yan gudun hijira a Najeriya da Sudan ta Kudu

February 17, 2017

Rashin samun taimakon da ake ware wa domin mutannen da rikicin Boko Haram ya tagayara a Najeriya, da batun yan gudun hijira a Sudan ta Kudu, na daga cikin batutuwan da suka dauki hankullin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2XmhB
Niger Flüchtlinge aus Nigeria
Hoto: DW/A. Cascais

Jaridar ta Tageszeitung ta yi tsokaci da cewa a jihar Borno akwai kungiyoyin agaji 126 wadanda suka ce suna aiki da sunan taimaka wa mutanen da suka gamu da ibtila'in rikicin Boko Haram, amma daga cikin wannan adadi kungiyoyi takwas ne kacal aka tabbatar a zahiri suna aikin taimakon bil hakki da gaskiya kamar yadda gwamnan jihar Bornon Kashim Shattima ya nunar.

A kasafin kudin Najeriyar na shekarar 2016 gwamnatin ta ware Naira biliyan 10 kwatankwacin Euro miliya 29 da dubu 400 domin kai agaji a sansanonin yan gudun hijira da ke arewa maso gabashin kasar. To amma shin su wanene suka sami kudin?  kuma me wannan ke nufi ga yunkurin da aka sa a gaba na taimaka wa mutanen da suka shiga halin tagaiyara sakamakon rikicin Boko Haram? Wannan damuwa ta sa wata kungiyar farar hulla a Najeriyar mai lakabin follow the money wato bin diddigi sau da kafa na kudaden da aka ware, amfani da manhajar WhatsApp domin samun rahotanni da kuma bayanai daga mutanen da abin ya shafa a kauyuka, su kuma wallafa bayanan a shafinsu na Internet.

Matsalar 'yan gudun hijira a Sudan ta Kudu

Bildergalerie Südsudan Der jüngste Staat der Welt versinkt im Chaos
Hoto: DW/J.-P.Scholz/A.Kriesch

A labarin da ta buga game da Sudan ta Kudu jaridar Neues Deutschland ta tabo batun yan gudun hijira ne na cikin gida a kasar. Jaridar ta ce bisa ga alkaluman Majalisar Dinkin Duniya, yakin basasar Sudan ta Kudu ya haifar da gagarumar matsalar 'yan gudun hijira a Afirka, inda mutane fiye da miliyan daya da rabi suka yi kaura daga Sudan ta Kudu a shekaru biyu da suka wuce tun bayan barkewar takaddama tsakanin shugaba kasar Salva Kiir da babban madugun 'yan tawaye Riek Machar a cewar hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya. Wannan adadi ya haura kashi goma cikin dari na jama'ar kasar a cewar jaridar ta Neus Deutschland. Kimanin kashi 60 cikin dari na yan gudun hijirar yara ne. Jaridar ta ce a yanzu Sudan ta Kudu ita ce kan gaba a yawan 'yan gudun hijira a Afirka.

Dan Kamaru ya lashe gasar fasaha ta Google

google homepage Bildschirm Lupe
Hoto: picture-alliance/Bildagentur-online/Schoening

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhinta ne akan matashi dan Kamaru Nji Collins Gbah, mai shekaru 17 da haihuwa wanda ya lashe gasar fasaha ta Google. Wannan ne dai karon farko da wani dan Afirka ya lashe gasar fasahar ta Google.  Jaridar ta ce Nji wanda ya fito daga Bamenda ya nuna basira da juriya da kuma sha'awarsa na samun cigaba, inda duk da kalubalen da ya fuskanta da hukumomi suka toshe hanyoyin sadarwa a yankin sakamakon rikicin da aka samu a bangaren kasar da ke amfani da harshen Ingilishi duk da haka ya dage domin kai wa ga wannan nasara. Duk da yabo da matashin ya samu daga bangarori daban-daban, a na ta bangaren gwamnatin har yanzu ba ta bada wani martani ba.