1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin da shugaban Iran ya yi game da Isra'ila ya janyo masa kakkausar suka a kasashen Yamma.

YAHAYA AHMEDOctober 27, 2005

Kiran da shugaba Mahmoud Ahmedinejad na Iran ya yi, na a kau da Isra'ila daga doron kasa, ya janyo wani ka ce-na ce da kasashen Yamma, wadanda ke yi mahunkuntan birnin Teheran kakkausar suka da kuma nuna bacin ransu.

https://p.dw.com/p/Bu4Z
Shugaba Ahmedinejad, yayin da yake kira a birnin Teheran, ga ragargaza Isra'ila da share ta daga doron Kasa.
Shugaba Ahmedinejad, yayin da yake kira a birnin Teheran, ga ragargaza Isra'ila da share ta daga doron Kasa.Hoto: AP

Kiran da shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad ya yi jiya a birnin Teheran, na a kau da Isar’ila daga doron kasa, ya janyo kakkausar suka daga kasashen Yamma. Shugaban dai ya yi kiran ne a cikin wani jawabin da ya yi wa taron masu adawa da Isra’ila a babban birnin kasarsa, inda ya kwatanta rikicin Gabas Ta Tsakiya tamkar wani gagarumin yaki tsakanin `yan mulkin mallaka na kasa da kasa da baraden bakin daga na duniyar musulmi.

Wannan kiran dai, ba wani sabon abu ba ne ga mahunkuntan birnin na Teheran. Tsohon shugaban addinin kasar ta Iran, marigayi Ayatullah Khomeini ma ya taba yin wannan kiran. Kuma a ganin shugaban kasar na yanzu, Ahmedinejad, duniya za ta iya ci gaba da harkokinta ba tare da yin la’akari da Amirka ko Isra’ila ba.

Tuni dai, Amirkan da Isra’ila ne suka fara mai da martani, inda suka bayyana cewa, yanzu Iran ta nuna wa duniya manufofin da ta sanya a gaba a zahiri. Sabili da haka ne kuwa ya kamata a dau duk wasu matakan da suka dace na hana wata samun tushenta daga birnin Teheran. A nahiyar Turai ma, kasashe da dama sun nuna damuwarsu ga kalamar da shugaba Ahmedinejad ya yi.

To amma masharhanta da dama na ganin cewa, ai wannan matsayin da Iran ta dauka ba wani abin mamaki ba ne. Tun lokacin juyin juya halin kasar da marigayi Aayatullah Khomeini ya jagoranci ne dai Iran ta nuna matsayinta na kin amincewa da wanzuwar Isra’ila. Har yanzu kuma, wannan matsayin na daya daga cikin muhimman jigogin ajandar siyasa na mahukuntan birnin Teheran, duk da cewa, an dade ba a ji irin kakkausan kalami kamar wadda shugaba Ahmedinejad ya yi ba. A lokacin mulkin shugaba Khatammi ma, sai da ministan harkokin wajen kasar, Kharrazi, ya bayyana cewa a ganinsa dai, Isra’ila haramtacciyar kasa ce, sabili da haka bai kamata a amince da ita ko a dama da ita a harkokin gamayyar kasa da kasa ba.

A nan Yamma dai, ana ganin Ahmedinejad ya mai da hannun agogo baya ne, inda ake tinkarar komawa zuwa farkon lokaci na juyin juya halin. Masu sukar lamiri da yawa na kasashen Yamma na yi masa kallon wani dan rikau ne, mai tsatsaurar ra’ayi, wanda kuma ba ya la’akari da sakamakon da kalamunsa za su iya haifar masa da ma kasarsa.

Shugaban Ahmedinejad kuwa, a nasa bangaren, ya yi wannan jawabin ne a daidai lokacin da ake samun hauhawar tsamari tsakanin kasarsa da Amirka da kuma nahiyar Turai, saboda rikicin da bangarorin biyu ke yi kan batun nan na makamashin nukiliyan Iran din. Su dai kasashen Yamman na zargin birnin Teheran ne da kokarin sarrafa makaman kare dangi. Ita ko Iran, ta dage kan cewa ba ta wata sha’awar mallakar makamn nukiliya. Tana kokari ne na samar wa kanta, tabbataccen tushe na makamashi isasshe.

A halin da ake ciki yanzu kam, kasashen Yamma za su shiga cikin wani halin zaman tsarguwa ne da Iran. A nasu ganin, duk wata kasar da ke kira ga ragargaza wata, ko kuma shafe ta daga doron kasa, to kamata ya yi a yi taka tsantsan da ita. Bisa dukkan alamu dai, Iran din za ta huskanci matsaloli wajen samun magoya baya a ketare a kan wannan batun.