Jiragen yakin Faransa sun kai sabon hari kan IS
November 17, 2015Talla
Jiragen yakin kasar Faransa sun sake kaddamar da wasu sabbin hare-hare a daren jiya washe garin wannan Talata a birnin Raqa cibiyar Kungiyar IS.
Ofishin ministan tsaron kasar ta Faransa wanda ya sanar da wannan labari ya ce jiragen yaki 10 ne sanfarin Mirage 2000 da Rafale da suka taso daga kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Jodan suka kaddamar da harin inda suka jefa bama-bamai 16 kan gurare daban-daban na birnin Raqa inda suka lalata wata cibiyar bayar da umarni da kuma wata cibiyar horas da mayakan kungiyar.