1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan ya kama da wuta a Borno

Abdoulaye Mamane Amadou
December 5, 2024

Jirgin sama mallakar kamfanin Max Air a Najeriya ya yi saukar gaggawa bayan da ya kam ada wuta a sararin samaniya jim kadan bayan tashi daga Maiduguri

https://p.dw.com/p/4nnkf
Air Canada Boeing 737 Max
Hoto: Darryl Dyick/empics/picture alliance

Mataimakin gwamnan jihar Borno Usman Kadafur na daga cikin fasinjoji akalla 100 da suka tsallake rijiya da baya, bayan jirgin Max Air da ke dauke da su zuwa Abuja ya kama da wuta a sararin samaniya, mintoci kalilan da tashin jirgin daga Maiduguri na jihar Boron Najeriya.

Karin bayani : Fargaba bayan faduwar jirgi marasa matuki a Nijar

Wasu fasinjojin da suka tsallake rijiya da baya, sun bayyana cewa jirgin ya fara rikicewa ne mintoci 10 da tashi, inda aka lura guda daga cikin jirgin ya fara kamawa da wuta nan take matukin jirgin ya yi kokari ya kashe injin din, tare da juyawa zuwa Maiduguri ya yi saukar gaggawa.

Karin bayani : Jirgin dakon kayan DHL ya yi hatsari a Lithuania

Babu wani fasinja ko daya da ya jikkata, sai dai akwai yiwuwar tsuntsu ne ya shiga injin din jirgin a cewar wasu ma'aikata. Mataimakin Gwamnan jihar Borno wanda ya ce dukkanin sun yi Sujada ta godiya ga Allaha, ya sake bin wani jrgin zuwa Abuja.