SiyasaGabas ta Tsakiya
An bude zirga-zirgar tsakanin Saudiyya da Katar
January 11, 2021Talla
Bayan jigilar fasinjar da jirgin kamfanin Qatar Airways ya yi ta sa'a daya zuwa Saudiyyar, ita ma Saudiyya din ta shirya tashin wani jirgin fasinja a wannan Litinin zuwa kasar Kasar din.
Kasashen biyu na yunkurin sasanta zaman doya da manjar da suka fara a shekara ta 2017, lokacin da Saudiyya ta zargi Katar da daukar nauyin ta'addanci, zargin da Katar ta musanta tana zargin Saudiyya da raina mata 'yancinta na matsayin kasa mai cikakken iko.