An samu hadarin jirgin sama a Sudan ta Kudu
November 4, 2015Talla
Rahotanni daga kasar Sudan ta Kudu sun nuna cewa fiye da mutane 20 sun hallaka lokacin da jirgin saman dakon kaya da ya tashi daga birnin Juba fadar gwamnatin kasar ya fadi. Jirgin saman ya fadi a kan hanyar zuwa Jihar Upper Nile da ke yankin arewacin kasar, kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar ya tabbatar.
Jirgin saman ya fadi a cikin dajin da kogin Nilo ya ratsa. Kawo yanzu ana ci gaba da tattara bayanai kan hakikanin abin da ya faru.