Jirgin saman soji ya fadi a Abuja
February 21, 2021Talla
Mutane shida ne da matuka biyu ke cikin jirgin wanda ke hanyarsa ta zuwa Minna jihar Niger a lokacin da ya yi hatsarin sakamakon matsala da injin.
Ministan sufurin Najeriyar Hadi Sirika wanda ya tabbatar wa DW labarin, ya ce babu wanda ya tsira da ransa.