SiyasaGabas ta Tsakiya
Jirgin sojin Isra'ila ya yi hatsari a tekun Mediterranean
January 4, 2022Talla
Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakin rundunar sojin Isra'ila ya yi hatsari a kusa da tekun Mediterranean a arewacin kasar. Sanarwar hukumomin sojin Isra'ila ta safiyar wannan Talata ta ce nan take matuka jirgin guda biyu sun rasa rayukansu a yayin da mutum na uku da ke cikin jirgin ya ji munanan raunuka.
Kawo yanzu ba a san musabbabin hatsarin ba. Sai dai bayan da ya kaddamar da bincike kan lamarin, shugaban rundunar sojin Isra'ila Amikam Norkin ya umurci a dakatar da horar da sojojin.