Jirgin yakin ruwan Jamus ya nufi Bahar Maliya
February 8, 2024Jamus ta bi sahun yunkurin dakile hare-haren mayakan na Houthi da a wannan rana ta alhamis jirgin ruwanta na yaki ya dau hanyar zuwa tekun Bahar Maliya domin haduwa da sauran dakarun kawancen kasashe na rundunar tsaro ta musamman da aka kafa da nufin murkushe mayakan na Houthi da ke ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa.
Kamfanin dillancin labarai na Jamus DPA ya jiyo daga majiyar diflomasiyya cewa EU ta amince da shirin jibge dakaru a tekun Bahar Maliya da gabar tekun Aden harma da sauran gabar ruwan da ke yankunan.
Karin bayani:-Bahar Maliya: Takaddamar Amurka da Houthi
Jirgin ruwan na Jamus na dauke da mutane 240 bayan da majalisar tarayyar Turai da majalisar dokokin Jamus suka amince da daukar wannan mataki, a cewar shugaban hafsan sojan ruwan Jamus Vice Admiral Jan Christian Kaack.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Burtaniya suka kaddamar da farmaki kan mayakan na Houthi.