1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump na jan kafa wajen mika mulki

Abdourahamane Hassane
November 17, 2020

Zababben Shugaban Amirka mai jiran gado Joe Biden ya sake gayatar Shugaba mai barin gado Donald Trump da ya gaggauta fara shirin mika masa  mulki.

https://p.dw.com/p/3lOE0
USA | Joe Biden designierter Präsident | Rede in Wilmington
Hoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Joe Biden ya yi gargadin cewar  jinkirin da Donald Trump din yake na kin ba da hadin kai wajen shirye-shiryen mika mulki na iya yin illa ga rayuwar al'umma. Biden ya bayyana haka ne a mahaifar sa a Wilmington sannan ya kara da cewar: ''wasu karin mutunan na iya mutuwa inda har aka ci gaba da samun jinkiri, jama'a za su mutu da corona, duk da ma cewar an samu alurar riga kafi.n Har ya zuwa yanzu dai Donald Trump ya ki amincewa da shan kaye a zaben kasar da ya gudana a cikin wannan wata.