SiyasaAfirka
Zaben Amirka: Democrat ta tabbatar da takarar Joe Biden
August 19, 2020Talla
Jiga-jigan jam'iyyar sun yi wannan ikirari ne a ranar Talata da daddare lokacin bikin tabbatar da Joe Biden a matsayin dan takarar Democrat a hukumance. Uwargidan dan takarar na Democract Jill Biden ta sha alwashin cewa mijinta ba zai ba Amirkawa kunya ba.
Joe Biden ya kasance mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Barack Obama daga shekara ta 2009 zuwa 2017, ya kuma samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta Democrat a bana ne bayan ya yi rashin nasarar samu a shekarun 1988 da kuma 2008.