John Kerry zai tattauna da shugabannin Isra'ila da Falasɗinu
March 31, 2014Talla
Kerry wanda ya isa a yau birnin Tel-Aviv, an shirya zai gana da firaminsta Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Ƙudus, da kuma jagoran falasɗinawa Mahamud Abbas a Ramallah, kafin ya isa a Brussel a gobe Talata idan zai halarci taron Ƙungiyar NATO.
Isra'ila dai ta ƙi ta saki wani rukunin na ƙarshe na fursunan Falasɗinu a ranar Asabar da ta gabata kamar yadda aka tsara a tattaunawar ta farfaɗo da zaman lafiya a yanki Gabas ta Tsakiyar. Tana mai cewar za ta sake sune kawai, idan Falasɗinu ta amince a ƙara tsawaita wa'adin tattaunwar ta gaba da gaba da nufin samun zaman lafiya wadda wa'adinta ke kawo ƙarshe a ranar 29 ga watan Afrilu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal