John Magufuli ya lashe zaben shugaban kasar Tanzaniya
October 29, 2015A wannan Alhamis Shugaban hukumar zaben Tanzaniya Damian Lubuva ya ayyana John Pombe Magufuli a matsayin wanda yayi nasarar zaben wanda aka dade ana dakon sakamakonsa.
"A hukumance ina sanar da sakamakon zaben shugaban kasar inda aka zabi Dr. John Pombe Magufuli a matsayin shugaban kasa da kuma Samia Suluhu Hassan a matsayin mataimakiyarsa."
Sai dai duk da cewar abokin karawar tasa Edward Lowassa ya ce sam bai amince da wannan sakamako ba, amma shugaban jam'iyyar ta hamayya wato Chadema ya bayyana cewar zabe dama ya gaji ko dai mutum ya samu nasara ko kuma ya ci kasa. Duk da cewar jam'iyyarsa ba ta samu nasara ba, ba damuwa, shi dai yana maraba da dukkan wani lamari da zai ciyar da kasar gaba.
"Ina mai ra'ayin cewar duk wata jam'iyya da za ta kawo wa kasar cigaba mai amfani to ina goya mata baya, ko daga wacce jam'iyya ce, don haka na yi na'am da wannan sakamako."
Zargin tabka magudin zabe
Idan dai an tuna a baya shugaban 'yan adawar ya yi kiran da a dakatar da bayyana sakamakon zaben wanda suka ce suna zargin gwamnati tare da hadin bakin hukumar zaben wajen tafka magudi. Zargin da hukumar ta musanta, a yayin da a hannu guda kuma aka soke zaben tsibirin Zanzibar mai takaitaccen 'yancin gashin kai daga kasar ta Tanzaniya. Sai dai shugaban babbar jam'iyyar adawar kasar ta CUF Seif Sharif Hamad wanda ke rike da mukamin shugaban tsibirin na Zanzibar da tun a farkon makon ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, ya yi tir da shi.
Shi dai zababben shugaban kasar mai shekaru 55 da haihuwa ya kasance tsohon malamin makaranta wanda daga bisani ya juye ya zama dan siyasa. Ya kuma shafe shekaru 38 yana zaman memba kuma mai biyayya ga jam'iyyar ta CCM. An zabe shi memba a majalisar dokokin kasar inda ya wakilici mazabar Biharamulo ta Gabas a shekara ta 1995, wanda kuma daga baya aka zabe shi a matsayin mataimakin ministan kula da ayyuka har zuwa shekara ta 2000.
A shekara ta 2005 a karkashin mulkin Shugaba Jakaya Kikwete aka nada shi ministan kula da kasa da gidaje har na tsawon shekaru uku. Daga nan kuma ya koma ma'aikatar kula kiwo daga shekara ta 2008 zuwa 2010, bayan kuma zaben shekara ta 2010 aka sake dawo da shi ma'aikatar ayyuka, mukamin da yake rike da shi izuwa yanzu da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban kasa.
Yabo game da ayyukan da ya yi a baya
Ya dai samu yabo matuka a mukaman da ya rike sakamakon jajircewarsa wajen ganin lamura sun tafi yadda ya kamata, inda har ake masa lakabi da Jembe, ma'ana mai kwazon aiki, sakamakon yadda ya tsaya wajen ganin kowanne bangare na kasar an gabatar da ayyukan cigaban al'umma.
Haka kuma ya kasance mutum ne da baya karbar cin hanci da rashawa ko kuma aikata wani abu da ka iya zamar masa matsala ta kowane fanni.
A lokacin da yake gabatar da yakin neman zabensa ya kan gaya wa mutane cewar fatansa shi ne ganin kowane bangare na al'ummar kasar shi ne a dama da ita a sha'anin mulki ba tare da fifita wata kabila ba.
Wani abu da yake bai wa jama'a mamaki a rayuwarsa shi ne mutum ne wanda yana da wahala ya manta wani abu da aka gaya masa, shi yasa ma y'an jarida ke muradin ganin sun tattauna da shi domin sanin wani abu a game da rayuwarsa.
Misali, ko a lokacin kaddamar da gangamin zaben shekara ta 2010, yan jarida sun tambaye shi adadin ayyukan da ma'aikatarsa ta kammala da wanda ake kan yi, in da nan take ya fadi adadin da kuma wuraren da aka gama aikin da wadanda ake gudanarwa, duk da cewar abubuwan na da yawan gaske.
Yanzu dai babban aikin da ke gaban sabon shugaban kasar wanda dama yana ta nanatawa a lokacin da yakin neman zabe shi ne batun kakkabe cin hanci da rashawa da bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma uwa uba raunin da ma'aikatan kasar ke da shi na rashin zuwa aiki a kan lokaci.