1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

John Magufuli ya zama shugaban Tanzaniya

Zainab Mohammed AbubakarNovember 5, 2015

An rantsar da sabon shugaban ne tare da mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan, wanda ke zama karo na farko da Tanzaniya ke nada mace a kan wannan mukami.

https://p.dw.com/p/1H0eS
Tansania Samia Suluhu und John Magufuli
Hoto: Getty Images/AFP/D. Hayduk

Mai shekaru 56 da haihuwa, Magufuli ya lashe zaben ranar 25 ga watan Oktoba yawan kuri'u sama da kashi 58 daga cikin 100, wanda ya kara ba wa jam'iyyar da ke mulki ta CCM damar ci-gaba da rike madafan iko.

Akasarin zaben dai ya tafi lami lafiya, sai dai 'yan adawa sun yi watsi da sakamakon kan zargin tabka magudi. A hannu guda kuma an soke zaben shugaban kasa a tsibirin Zanzibar mai kwarya kwaryar 'yancin kai, sakamakon zargin tabka magudi.

Shugaban Tanzaniya mai barin gado Jakaya Kikweti, yanuna farin cikinsa da mika ragamar mulki bayan kammala wa'adinsa biyu na shekaru 10.

Magufuli ya kasance tsohon malamin makaranta, kana ya tafiyar da wata kungiya dake yaki da cin hanci da rashawa, kafin ya lashe kujerar shugaban kasar bayan doke abokin takararsa kuma tsohon fraiminista Edward Lowassa, wanda ya samu kashi 40 na yawan kuri'un da aka kada.